Kungiyoyin Kwadago da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa tare da kudurin ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum na tsawon mako guda don sake bai wa kwamitin mafi karancin albashi na kasa dama har a samu a cimma matsaya ta karshe.
Bayanin hakan ya fito da yammacin ranar Litinin a karshen taron da kungiyoyin Kwadago na NLC/TUC su ka gudunar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, a sakamakon bukatar da ake da ita na samun damar ci gaba da tattaunawa da kwamitin da ke kula da mafi karancin albashi na kasa kan sabon mafi karancin albashi.
- Da Ɗuminsa: An Rufe Ƙofa Tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago Da Sakataren Gwamnatin Tarayya
- Yajin Aiki: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Rufe Filayen Jirgin Saman Legas Da Abuja
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa a ranar Litinin mambobin kungiyar kwadago ta kasa NLC da TUC suka shiga yajin aikin gama-gari a kasa baki daya, domin neman amsa bukatar su ta neman karin mafi karancin albashin ma’aikata da kuma sauya farashin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan. wanda ya gurgunta ayyukan gwamnati da masana’antu masu zaman kansu a fadin Nijeriya.
A wata sanarwa da aka fitar a karshen taron da aka gudanar da ministan yada labarai da takwaransa na kwadago da samar da ayyuka, Mohammed Idris da Nkiruka Onyejeocha, daga bangaren gwamnatin tarayya, da shugabannin NLC da TUC, Joe Ajaero da Festus Osifo suka amince da shi.
A taron an amince da wasu kudurori guda hudu a matsayin hanyar kawo karshen takaddama kan karin albashin.
“Shugaban kasa, ya kuduri aniyar biyan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa da ya haura N60,000;
“Saboda abubuwan da suka gabata, kwamitin zai ci gaba da gana wa a cikin mako a kullun har zuwa lokacin da za a cimma matsaya ta karshe kan mafi karancin albashi na kasa;
“Babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa a sakamakon shiga yajin aikin,” Cewar yarjejeniyar gwamnati da kungiyoyin kwadago.