Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta sanar da cewa, za ta yi Zanga-zanga a fadin Nijeriya baki daya daga ranar 26 zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2022 don ta tilasta wa Gwamnatin Tarayya Lalubo mafita kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’in kasar nan(ASUU) da yaki-ci-yaki-cinyewa.
In ba a manta ba, ASUU ta tsunduma yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 saboda Gwamnatin taki wanzar da yarjejeniyar dake tsakaninta da kungiyar Malaman wacce bangarori biyun suka cimma a shekarun baya.
NLC a baya ta bai wa Gwamnatin wa’adin kwanaki 21 don lalubo mafita kan rikicin da yaki-ci-yaki-cinyewa a tsakanin Gwamnati da ASUU, inda a yanzu, wannan wa’adin na NLC ya cika ta kuma yanke shawarar tsunduma cikin Zanga-zangar.
Ganin cewa wa’adin na NLC ya cika ne a cikin sanarwar da shugabanta na kasa Ayuba Wabba ya fitar ya bayyana cewa, rassan NLC da ke daukacin jihohi 36 har da Abuja za su shiga Zanga-zangar takin zuwa wuraren ayyukansu aduk fadin Nijeriya.