Tsohon Mataimakin shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya alakanta laifin yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ke yi kan sakacin Ministan Ilimi, Adamu Adamu.
Atiku ya bayyana hakan ne a hirar da gidajen rediyo suka yi da shi a ranar Talata a Kano, Atiku ya zargi Gwamnatin Tarayya da rashin daukar yajin aikin jami’o’in da muhimmanci, shi ya sa ba ta mayar da hankali ta kawo karshensa ba.
“Na tattauna da Malam Ibrahim Shekarau, wanda tsohon Ministan Ilimi ne, ya bayyana min cewa a lokacin da aka nada shi ministan Ilimi, ASUU na cikin yajin aiki, amma cikin sati uku aka shawo kan lamarin aka samu fahimtar juna suka dawo bakin aiki.
“Akwai rashin kwarewa a tattare da ministan Ilimi – na yanzun, sabida shike da alhakin nemo mafita ta yadda ya dace, wacce za ta kai kowa ga tudun na tsira.” Inji Atiku.
In ba a manta ba dai, Atiku ya ziyarci Jihar Kano ne domin karbar tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa da suka sauya sheka daga Jam’iyyar NNPP zuwa PDP.