Rahotannin sun ruwaito cewa, kwanan nan masu gabatar da kara a kasar Turkiyya sun sake bada izinin cafke wasu mutane 25, da ake zargi da aikata laifin kai farmaki kan wata mujami’a a birnin Istanbul, ciki har da wani dan asalin kasar Sin, wanda ya sauya zuwa dan kasar Turkiyya. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya jaddada a yau Alhamis cewa, kungiyar ETIM wato East Turkestan Islamic Movement ta aikata ayyukan ta’addanci da dama a ciki da wajen kasar Sin, kuma ita ce kungiyar ‘yan ta’adda da gwamnatin kasar Sin ta ayyana bisa doka, kana kungiya ce da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya gami da gwamnatin Turkiyya suka ayyana sunanta cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda. A cewarsa, yakar kungiyar ETIM, muhimmin abu ne da kasar Sin ke mayar da hankali a kai, yayin da take kokarin yaki da ayyukan ta’addanci, kana babban nauyi ne dake wuyan kasa da kasa.
Har wa yau, a jiya Laraba, sassan kula da tsaron yanar gizo ta Intanet na kawancen Five Eyes Alliance sun yi gargadin cewa, kungiyoyi masu kutsen intanet dake samun goyon-baya daga gwamnatin kasar Sin, sun kutsa cikin kafofin yanar gizo ta intanet da suka shafi muhimman ababen more rayuwar al’umma da dama na Amurka, don shirye-shiryen kai farmakin intanet. Game da wannan batu, Wang Wenbin ya ce, kasar Sin na matukar adawa da zargin da Amurka da sauran wasu kasashen dake cikin Five Eyes Alliance suke yi mata ba gaira ba dalili. Ya ce babban dalilin da ya sa kawancen Five Eyes Alliance ya dade yana shafa wa kasar Sin bakin fenti shi ne, yadda yake jirkita gaskiyar al’amura, wato kawancen shi ne kungiyar masu leken asiri mafi girma a duniya, inda ya ce Amurka ce kasar dake kutsen intanet mafi muni a duniya. (Murtala Zhang)