Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da kashe Naira miliyan 580.5 don siyan motocin sulke guda hudu ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen taron majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja a ranar Laraba.
Ya ce: “A yau, ofishin babban mai shari’a na tarayya, wato ma’aikatar shari’a ta tarayya, ta gabatar da wata takardar kudiri kan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA dake karkashin kulawar ofishin babban mai shari’a.
“Makasudin rubuta wannan takarda shi ne neman amincewar majalisar don bayar da kwangilar samar da motocin tsaro na musamman guda hudu masu dauke da kujeru 14 na hukumar NDLEA.”
Ministan ya ce an dauki matakin sayo motocin sulken ne domin karfafawa da kuma kare rayukan ma’aikatan NDLEA dake aiki tukuru kuma suna samun nasara mai ban mamaki.