A yau Litinin aka samu barkewar yamutsi a tsakanin ‘yan majalisar dokokin jihar Benuwai, inda wakilan suka ringa musayar baki wajen zabar sabon shugaban majalisar.
Burfushin hatsaniyar dai ta fara kunno kai yayin kaddamar da majalisar jihar ta 10.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 Da Sojoji 2 A Jihar Benuwe
- Buhari Ya Yi Kira A Kawo Karshen Kashe-Kashe A Benue
‘Yan majalisar su 32 sun samu damar zabar sabon shugaban majalisar da kuma mataimakinsa.
An dai mayar da Kujerar shugaban majalisar ce, zuwa karamar hukumar Gboko da ke a shiyyar Benuwai ta arewa maso yamma.
Gwamnan jihar, ya fito ne daga karamar hukumar Vandeikya da ke shiyyar Benuwai ta arewa maso gabas, inda kuma mataimakinsa, ya fito daga karamar hukumar Otukpo da ke gundumar Benuwai ta kudu.
‘Yan takarar mukamin na shugaban biyu sune, Becky Orpine wacce ke wakiltar mazabar Gboko ta gabas, sai kuma Aondonna Hyacinth Dajo, da ke wakiltar mazabar Gboko ta yamma.
Orpine na cikin magoya bayan bangaren APC tsagin George Akume da ke marawa baya, kuma ta na da goyon bayan kwamitin zartarwa na APC reshen jihar.
Har ila yau Orpine ita ce ‘yar takara mace daya tilo da aka zaba a majalisar ta 10.
Daukacin magoya bayan ‘yan takarar sun bukaci a soke zaben kan zargin tabka magudi.