Akalla jami’an tsaro uku ne suka mutu a ranar Litinin bayan da ‘yan kunar bakin wake suka kai hari kan hedikwatar rundunar jami’an tsaro ta cikin gida (FC) da ke Peshawar, arewa maso yammacin Pakistan.
A cewar jami’an ‘yansanda da jami’an tsaro, maharan uku sun kusa kutsawa cikin harabar hedikwatar yayin da ɗaya daga cikinsu ya tayar da bam a bakin kofar, sauran kuma suka yi yunkurin kutsa da karfi.
ADVERTISEMENT
- Sin Da Afrika Ta Kudu Sun Fitar Da Shawarar Hadin Gwiwa Ta Goyon Bayan Zamanantar Da Kasashen Afrika
- Tinubu Ya Umarci A Janye Ƴansandan Da Ke Tsaron Manyan Mutane
Jami’an tsaro sun yi gaggawar harbe su, inda suka hana maharan shiga cikin sansanin.
Fashewa bam da harbe-harben da suka biyo baya sun yi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan FC uku tare da jikkata wasu akalla biyar, in ji hukumomin tsaron kasar.














