Ga dukkan alamu, masu adawa da ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben 2023 na ci gaba da matsa kaimi da tayar da jijiyoyin wuya da kumfar baki musamman game da rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 2023.
Mafi yawancin ‘yan adawa wadanda ba su ji dadin sakamakon zaben ba, sun bukaci kar a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa har sai kotu ta kammala shari’ar da ke gabanta, saboda a cewarsu, zaben na cike da magudi.
- Waiwaye Game Da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida Ta Duniya
- Montana Ta Zama Jihar Amurka Ta Farko Da Ta Haramta TikTok
Haka kuma sun bukaci a kafa gwamnatin rikon kwarya idan wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shude.
Masu shigar da karar sun kuma bukaci a fitar da sanarwar tsawaita wa’adin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari har sai an tantance wanda zai gaje shi kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
A yayin zaman da aka yi a ranar Litinin, lauyan wadanda suka shigar da kara, Chuks Nwachukwu, ya shaida wa kotun cewa sun shigar da karar ne domin kotun daukaka kara ta hana duk wani tsarin mika mulki.
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Nwachukwu ya bayyana cewa zababben shugaban kasar bai cika dukkan abubuwan da ake bukata kafin zama shugaban kasa.
Ya ce hujjar cewa shugabannin da suka shude sun fuskanci koke-koke bayan an rantsar da su kan karagar mulki.
A cewarsa, shuwagabannin da suka shude sun cika dukkan abubuwan da ake bukata kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Ya kara da cewa, “Suna bukatar dukkan akwatunan da takarda zabe da aka yi amfani da su lokacin zabe. Amma kundin tsarin mulkin kasar bai dauki Tinubu a matsayin wanda ya dace ya zama shugaban kasa ba, saboda bai cika sharudda ba.”
Ya ce shi bai damu da masu ra’ayin cewa za a yi tazarce idan ba a rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, saboda tsarin mulki ya bai wa shugaban kasa mai ci damar kula da al’amuran kasa har sai wanda ya cancanta ya karbi mulki.
Nwachukwu ya ce, “Muna tabbatar da cewa babu wanda zai fahimci manufarmu. Masu shigar da kara na zaben suna ta kokawa a tsakaninsu kan wanda ya kamata ya yi nasara. Ba mu sha’awa a kan wanda zai yi nasara.
“Abin da muke sha’awar shi ne duk wanda za a rantsar da shi ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka jefa a jihoji ciki har da Abuja idan kuma ba a samu ba, to babu wanda za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu.
Ita kuwa jam’iyyar LP ta bayyana cewa ya kamata a soke zaben shugaban kasa na 2023.
Jam’iyyar ta yi kira da a soke zaben shugaban kasar ne bisa ce-ce-kucen da ake yi dangane da kashi 25 na kuri’un da aka kada a jihohin Nijeriya ciki har da Abuja, babban birnin tarayya.
Babban mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Obi-Datti, Yunusa Tanko, ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani kan karar da ke neman a dakatar da rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar Nijeriya.
Tanko ya bayyana cewa jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, na sa ran ganin yanayin da kotu ta amince a rantsar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, har sai an zabi shugaban kasa nagari.
Ya ce, “Abin da na sani shi ne, za a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu idan har muka kasa samun nasara a kotun sauraron kararrakin zabe, rantsuwar za ta shafi shugaban kasa ne kawai. Wannan yana cikin sashe na 146 (2) na kundin tsarin mulki.
“Addu’armu ita ce a soke zaben, a kuma bayyana cewa babu shi. Wannan matsayi ya kasance ne tun da dan takarar APC bai samu kashi 25 a jihohin Nijeriya ciki har da Abuja. Idan an fayyace shi sosai, ya ba da ikon sashe na 146 na kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ce “Idan babu shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne zai karbi ragamar mulki”. Idan har shari’ar nan ta tafi yadda muke addu’a, abin da ake nufi shi ne Lawan zai karbi ragamar shugabancin tarayyar Nijeriya.
“Idan kuma Lawan bai dawo a matsayin shugaban majalisar dattawa ba ta 10 ba, dole ne ya mika wa zababben shugaban majalisar dattawa da za a kaddamar a watan Yuni, sannan zai bukaci a ba shi watanni tara domin gudanar da sabon zaben shugaban kasar. Haka ya kamata domin guje wa rudani a ko’ina.”
Sai dai kuma, rundunonin tsaron Nijeriya musamman na soja da ‘yansanda sun yi gargadi ga masu neman kawo rudani game da mika ragamar mulki a karshen watannan, suna masu cewa za su dauki matakin ba-sani-ba-sabo a kan ko ma waye da ke neman yin kafar ungulu ga shirin na mika mulki.
Rundunar sojojin Nijeriya da babban sufetan ‘yansandan Nijeriya, Usman Baba sun gargadi ‘yan siyasar da ke kokarin kawo rudani a kasa gami da kokarin kawo cikas ga bikin rantsar da sabon zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
Babban daraktan yada labarai na shalkwatar tsaro ta kasa, Bigediya Janar Tukur Gusau ya gargadi kungiyoyin da ke barazanar hargiza bikin rantsarwar da yunkurin lalata tsarin dimokuradiyyar da Nijeriya ke kai da su janye domin hukumomi ba za su lamunci hakan ba.
Haka nan shi ma Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya yi barazanar kawar da duk wani yunkuri da zai shafi matsalar tsaron kasa, ya kuma gargadi masu yunkurin kawo cikas da ka da su fara, don kuwa sojoji za su gama da su.
A nata bangaren, rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ce tana nan tana sanya idanu kan ’yan siyasar da ke kokarin kawo tsaiko ko kuma cikas game da rantsar da sabuwar gwamnatin a ranar 29 ga watan Mayu.
A wani taron manema labarai a shalkwatarsu, Babban Sufeton ‘Yansandan Nijeriya, Usman Baba ne ya bayyana cewa sun lura da wasu ‘yan siyasar da sakamakon zaben 2023 bai yi musu dadi ba na yin kalamai na tunzura jama’a, wanda hakan ka iya zama barazana ga bikin rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu da muke ciki.
“Rundunar ‘yansandan Nijeriya tare da hadin gwiwar jami’an tsaron leken asiri na kasa, suna sanya idanu sosai kan ayyukan wadannan jiga-jigan ‘yan siyasan da ma sauran wadansu marasa kishin kasa, wadanda a ko da yaushe suke burin ganin kasar ta fada cikin hali na tashin hankali da rashin zaman lafiya.
“Jami’an tsaro ba za su lamunci irin wadannan furuci da ka iya jefa kasar nan cikin rudani ba, duk wani dan siyasa da ya yi kunnen uwar shegu da gargadin, zai fuskanci fushin hukuma.” In ji shi.