Kungiyar As’habul Kahfu Warraqeen reshen jihar Bauchi ta sha alwashin daukaka kara dangane da hukuncin kisa da wata kotun shari’a ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a kwanakin baya.
A wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin ta yi watsi da hukuncin da alkali Ibrahim Sarki Yola ya yanke tare da misalta hukuncin a matsayin wanda ke cike da kura-kurai da kuma son zuciya a ciki.
Da ya ke karanta matsayarsu ga ‘yan jarida a shalkwatar ‘yan jarida da ke Bauchi (NUJ), Abdullahi Musa, Kakakin kungiyar, ya ce, da gangan Alkalin ya sauya batutuwan da suke akwai domin kaiwa ga matakin yanke hukuncin kisa ga malamin nasu.
Kungiyar ta zargi gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kitsa komai domin cimma manufarsa na dakile aniyar Abduljabbar Kabara bisa sukarsa da yake yi kan rashawa da cin hanci.
Musa ya ce, “Mun cimma matsar daukaka kara ne zuwa kotun sama domin neman hakki ta hanyar shari’a, domin kwata-kwata ba mu amince da hukuncin Ibrahim Sarki Yola ba; kuma abubuwan da aka yi wa malaminmu ya saba wa dokokin kare hakkin jama’a musamman dokar ‘yancin yin addini yadda mutum ya fahimta kamar yadda ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya.”
“Muna sane da wasu Malamai da suke adawa da Abduljabbar wadanda suka aikata laifuka na batanci da dama a wa’azozi da jawabansu amma babu wani abun da aka musu suna kan cigaba da wa’azozinsu ba tare da musgunawa ba.”
Kungiyar ta jero wasu da ta zarga da cewa su ma sun taba yin batanci da suka hada da Qaribu Kabara, Abdulrazak Yahya Haifan, Abbas Jega, Jalo Jalingo, Ahmad Gumi, Abdulwahab Abdullah da Sani Rijiyar Lemo amma babu wani da ya tuhumesu “Saboda su na kusa ko tare da masu mulki, su na nan a cikin ‘yancinsu a yayin da mu kuma shugabanmu wanda babu laifin da ya yi yana kan fuskantar shari’a.”
A cewarsu, zargin batanci da ake yi wa Abduljabbar Nasiru Kabara babu komai a ciki illa salon yakarsa da kokarin kawo karshensa hadi da bata masa suna ta kowace hanya da wasu wadanda ba su jin dadin wa’azinsa ciki har da gwamna Ganduje suka yi, “Duk wadannan abubuwan tsararru ne. Haka suka tsara domin cimma manufofinsu da ke boye.”
“Tun da farko mu ba mu amince da hukuncin ba, saboda mun yi imanin cewa gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu Malamai a jihar da aka sani na tsawon lokaci suke yakar Abduljabbar ne suka kitsa hakan ta hanyar masa karya da qage gami da jingina masa laifin batanci wanda kai tsaye sharri ne. Su kuma suka juya shaidu har aka kawo wannan matakin,” kungiyar ta yi zargi.