’Yan Banga sun ceto wasu mutane uku da ’yan bindiga suka sace a Jihar Taraba.
An gano waɗanda aka sace a mafakar ’yan bindigar da ke Eutse Kaehalla, a kan hanyar Minda a Ƙaramar Hukumar Lau.
- Dabarun Kasar Sin Na Iya Kawo Karshen Yunwa A Duniya
- Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
Da yake sanar da nasarar ceton mutanen a ranar Talata a Jalingo, wani shugaban ‘yan bangar ya ce jami’ansu sun kai farmaki sansanin ’yan bindigar, inda suka yi artabu da su, suka rinjaye su, kuma suka tilasta suka gudu.
Mutanen da aka ceto sun haɗa da Alhaji Umaru Abdullahi mai shekaru 50, Idi Bello mai shekaru 24, da Abubakar Adamu mai shekaru 45.
Da yake bayar da labarin halin da suka shiga, Abdullahi ya ce an sace su ne a gidajensu da tsakar dare, kuma an tsare su cikin mawuyacin hali.
“Sun zo da tsakar dare ɗauke da bindigogi, suka tafi da mu, suka ɗaure mu, tare da barazana cewa idan ba mu bi umarninsu ba za su kashe mu,” in ji shi.
Adamu, wanda yake fama da ciwo saboda dukan da aka yi masa, ya roƙi gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga.
Samamen da aka kai ya biyo bayan wani hari da aka kai garin Yelwa a ranar 15 ga watan Maris, inda aka kashe mutane biyu, aka kuma sace wasu uku.
Shugaban ayyuka na ‘yan bangar, Muniru Bello Abubakar, ya tabbatar da cewa ’yan bindiga na amfani da bayanan sirri daga mutanen cikin gari don samun bayani kan waɗanda za su sace da kuma hanyoyin kauce wa jami’an tsaro.
Ya gargaɗi masu taimaka wa ’yan bindiga da cewa za a ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp