Hedikwatar tsaro ta karyata ikirarin cewa ‘yan bindiga sun karɓe wani sansanin horo a jihar Neja.
A ranar Talata ne Majalisar Dokokin Jihar Neja ta nuna damuwa, inda ta yi zargin cewa, ‘yan bindiga sun mamaye sansanin sojoji da ke karamar hukumar Kontagora da wasu sassan karamar hukumar Mariga.
- Mene Ne Burin Amurka Wajen Sake Yada Jita-Jitar “Barazanar ‘Yan Leken Asirin Kasar Sin”
- Kotu Ta Ɗaure Wani Mutum Kan Zargin Cin Mutuncin Limami A Kano
A wani kuduri mai matukar muhimmanci ga jama’a, Abdullahi Isah, mai wakiltar mazabar Kontagora II, ya bayyana cewa, biyo bayan mamaye sansanin horar da sojoji da ‘yan bindiga suka yi, manoma daga yankuna fiye da 23 da ke kusa da sansanin sun tsere sun bar yankin saboda yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa.
Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Daraktan ayyukan yada labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya yi karin haske da cewa, duk da cewa ‘yan bindiga na gudanar da ayyukan su a wadannan yankuna, amma babu wani bangare na sansanin horon da ke karkashin ‘yan bindigar.
Buba ya bayyana cewa, hare-haren da sojoji suka kai a yankin ya hana ‘yan ta’addan samun damar gudanar da ayyukansu yadda suke so.