Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan bindiga ke tururuwa zuwa jiharsa bayan koro su daga malwabtan jihohi.
Gwamnan ya ce jami’an tsaro sun lura da karuwar ‘yan bindiga a karamar hukumar Karu, wadda ke da nisan kasa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin kasar.
“Mun lura da tarin ‘yan bindigar da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke karamar hukumar Karu.
“Kazalika, mun ga wasu daga cikinsu a kananan hukumomin Wamba da Toto.”
Haka nan gwamnan ya ce sun yi nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja bayan mayakan Boko Haram suka balle shi.
Wasu mazauna yankunan da hwamna Sule yake magana sun shaida wa BBC Hausa cewa sun shaida karuwar satar mutane a yankunan nasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp