Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe shugabar matan jam’iyyar Labour Party (LP) ta karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna, Misis Victoria Chintex.
Sakataren Yada Labarai na LP a shiyya ta 3, Edward Simon Buju, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana cewa mijin mamaciyar ya samu raunukan harbin bindiga a harin da aka kai musu a ranar Litinin a gidan su.
A cewarsa, “Iyalan Kudancin Kaduna (Shiyya ta 3) na jam’iyyar LP, suna mika ta’aziyya ga shugabanni da Excos na jam’iyyar Labour ta karamar hukumar Kaura bisa rasuwar mahaifiyarmu, ‘yar uwarmu, Misis Victoria Chintex, shugabar mata ta karamar hukumar Kaura. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbe ta a ranar Litinin a gidanta da ke Kaura.
Ya yi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar Labour daga kowace mazaba da kananan hukumomi da jiha da kuma na kasa baki daya da su yi musu addu’a a irin wannan mawuyacin lokaci da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp