‘Yan bindiga sun harbi fasinjoji biyu a kan hanyar Kontagora zuwa Tegina a Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun tare hanya da nufin yin garkuwa da mutane, amma direban motar ya yi saurin juya motar ya gudu.
- Kasar Sin Daya Ce Daga Cikin Kasashen Duniya Da Aka Amince Da Su a Matsayin Mafi Zaman Lafya
- Likitoci Masu Neman Ƙwarewa Sun Fara Yajin Aikin Ƙasa A Nijeriya
Sai dai ‘yan bindigar sun bi motar da harbi, inda fasinjoji biyu da ke gaban motar suka samu rauni a ƙafarsu.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce harin ya auku da misalin ƙarfe 12:15 na dare lokacin da maharan suka yi ƙoƙarin tare wata mota mai lamba MAK 238 XA a Tudun-Fulani.
“Direban ya yi nasarar tserewa, amma sun harbi motar, inda Zakari Benjamin da Samaila suka samu raunuka a ƙafafu,” in ji shi.
‘Yansanda daga Kontagora sun isa wajen da abin ya faru, sannan suka kai waɗanda suka ji rauni asibiti.
Abiodun ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa wajen, amma ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji.
Ya kuma shawarci direbobi da su guji yin tafiya cikin dare.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp