Wasu ‘yan bindiga da ba san ko su wane ba sun kai hari cocin St. Moses Katolika a Robuh, a Unguwan Aku a Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
‘Yan bindigar sun kashe akalla mutane uku tare da sace wasu da dama.
- Nasarar Oyebanji Ta Jadadda Yadda Ake Son APC — Buhari
- Tun Muna Kanana Aka Dora Mu A Kan Kyakkyawar Tarbiyya —Dakta Zahra’u
LEADERSHIP Hausa, ta gano yadda aka kai daya daga cikin wadanda suka ji rauni asibitin St. Gerald Katolika da ke Kaduna don ba shi kulawa.
Wakilinmu ya rawaito cewar ‘yan bindigar sun kai harin ne cikin dandazonsu, inda suka dinga hare a iska kafin daga bisani su budewa masu ibadar wuta, wanda hakan ya yi ajalin mutane uku sannan wasu da dama suka ji rauni.
‘Yan bindigar sun fasa shaguna da dama a yankin inda suka jidi kayan abinci da yawa.
Kwamishinan tsaron cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mataimakiyar gwamnan Jihar, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana bacin ranta sannan ta jajantawa wadanda harin ya rutsa da su.
Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni rundunar ‘yan sandan jihar ta shiga bincike don ceto wadanda maharan suka sace.