Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan tawagar jami’an ‘yansanda a kusa da iyakar Jihohin Nasarawa da Benuwe, inda suka jikkata ɗaya daga cikin jami’an.
Yayin musayar wuta tsakanin jami’an ‘yansandan da ‘yan bindigar, maharan sun harbe wani farar hula da ke zaune a kusa da yankin da harin ya faru inda ya baƙunci lahira nan take.
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka ‘Yan Sa-kai Sama Da 70 A Filato
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tare jami’an ‘yansandan ne da misalin ƙarfe 10:55 na daren ranar Talata, a yankin Kadarako da ke Ƙaramar Hukumar Keana ta Jihar Nasarawa, inda cikin gaggawa suma jami’an suka fuskanci maharan tare da mayar da martani don korarsu.
Kakakin Rundunar ‘Yansandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya bayyana cewa jami’an sun arangama da ‘yan bindigar ne yayin da suke fitowa daga dazukan jihar Benue, inda sakamakon hakan alburusai da ‘yan bindigar suka harba ya sami wani farar hula da ke kusa da wurin har ya rasa ransa.
A cewar SP Nansel, an garzaya da jami’in da aka jikkata zuwa cibiyar kula da lafiya da ke Kadarko don ba shi kulawa na gaggawa, kafin daga bisani a mayar da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya da ke Lafia, inda ake ci gaba da lura da shi.
Ya mika saƙon ta’aziyyarsa Kwamishinan ‘Yansandan Jihar, Shetima Jauro Mohammed, ga iyalan mamacin tare da tabbatar da cewa an ƙaddamar da bincike mai zurfi tare da shiga farautar waɗanda suka aikata harin domin a cafke su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp