Wani masani kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, Buhari Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda kashe-kashe da sace-sacen jama’a ke sake tabarbarewa, inda ya zargi cewa sama da kauyuka 400 ne ke karkashin ikon ‘yan ta’adda.
A wata hira ta musamman, Abubakar ya yi mamakin dalilin da ya sa shugaban kasa Bola Tinubu ke tura rundunar soji zuwa Jamhuriyar Nijar, maimakon mayar da hankali kan barazanar tsaro da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
- Yanzu-Yanzu: Masallacin Fadar Sarkin Zazzau Ya Rufta Da Mutane Yayin Sallar La’asar
- Kofin Duniya: Abin Da Ya Biyo Bayan Cire Nijeriya Daga Gasar
A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohi su yi taka tsan-tsan wajen ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara, domin ‘yan fashin sun kara karfi fiye da da.
Ya kara da cewa, “Duk wanda ya yi riya cewa komai ya daidaita a jihar Zamfara, yana yaudarar kansa ne, domin mazauna garin ba suma barci cikin salama sama da shekaru goma,” in ji shi.
Ya ce, bisa kididdigar da aka yi, akalla kauyuka 400 ne ke hannun ‘yan bindiga a jihar.
“’Yan ta’addan sun kafa gwamnatinsu a wadannan yankunan, kuma su ne suke yanke shawarar abin da zai faru da abin da ya kamata a yi a cikin al’ummomin da suke rike da su.
“Mutanen yankin sun san wadannan ‘yan fashi da maboyarsu amma ba za su iya magana ko fallasa su ba saboda fargaba, ‘yan bindigar sun sha gargadin kada su yi magana da wani dan jarida, idan ba haka ba za a kai musu hari.
A cewarsa, tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya na kan wuyan gwamnatin tarayya ba gwamnatin jiha ba kamar yadda mutane da yawa suka fahimta.
“Gwamnatin Jihohi na ba jami’an tsaro kayan aiki ne kawai don ba su damar gudanar da ayyukansu na tabbatar da rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa cikin sauki.
“Ko shakka babu jihar Zamfara ta zama mamayar ‘yan fashi a fadin kasar nan, yawan kashe-kashe da garkuwa da mutane da fyade ya zama ruwan dare.
“Akwai bayanai sun nuna a fili cewa akwai dubban zawarawa da marayu da ke yawo a kan tituna ba tare da wata manufa ba saboda ‘yan fashi da suka kashe mazajensu da iyayensu, wanda hakan ya sa suka zama almajirai da karuwai.
“Muna rayuwa cikin wani mummunan hali kamar ba mu da gwamnati ko jami’an tsaro a jihar kuma gwamnatoci da shugabannin tsaro suna kallo kamar babu abin da ke faruwa.
Abubakar ya ci gaba da bayanin cewa gwamnatin tarayya da na jihohi ba za su iya dakatar da wadannan kashe-kashe da sace-sacen mutane da fyade ba, idan ba a dauki tsauraran matakai ba, yana mai nuni da cewa akwai masu fada a ji a cikin wadannan munanan ayyuka, yana mai cewa ‘yan fashin ba su kadai suke yi ba.
Ya shawarci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su farka daga barcin da suke yi, su magance tsatsauran ra’ayi da duk wanda ke da hannu a cikin ta’addanci.
“Ayyukan ‘yan fashi sun jawo asarar dubban rayuka da karancin abinci yayin da manoma ba sa gudanar da ayyukansu na noma a jihar.”