Tawagar ‘yan wasa ta kwallon kafar mata ta dawo gida bayan rashin nasara da suka yi a hannun kasar Ingila a wasan faradda da kasashen suka fafata a gasar cin kofin duniya da a yanzu haka take gudana a kasashen Australia da New Zealand.
Nijeriya ta fito a cikin rukunin da ya hada kasashen Kanada da Jamhuriyar Irland da kuma mai masaukin baki Australia, kuma duk da haka ta samu damar fitowa daga cikin rukuni a mataki na biyu bayan ta samu nasara a wasa daya, sannan ta yi canjaras a wasanni biyu wanda hakan ya sa ta hada maki biyar.
- Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido
- Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
Sai dai ta yi rashin nasara a wasan da tawagar ta kece raini da tawagar Ingila, wadda ta doke Super Falcons din ta Nijeriya a bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan an tashi daga wasan babu kasar da ta zura kwallo a ragar ‘yar uwarta.
Wannan shi ne karo na tara da tawagar Nijeriya take zuwa gasar cin kofin duniya tun daga shekara ta 1991 da ta fara zuwa, inda tawagar ta buga wasanni 29 tun daga shekarar da ta fara zuwa gasar ta samu nasara a wasanni biyar ta yi canjaras sau biyar, sannan ta yi rashin nasara a wasanni 19, sai aka zura mata kwallaye 65 ita kuma ta zura guda 23.
Sai dai duk da haka Nijeriya ce kasa ta farko daga Nahiyar Afirka da ta je wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da kuma gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympic.
Har ila yau, Nijeriya ce tafi kowacce kasa a Nahiyar Afirka yawan lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta mata, inda ta lashe gasar sau 11 a tarihi.
Kin Biyan Albashi Da Alawus Din ‘Yan Wasa
Har yanzu ‘yan wasan ba su karbi albashin da suke bin hukumar kwallon kafa ta kasa ba da kuma ragowar hakkokinsu wanda tuni wasu daga cikin tsofaffin ‘yan wasan Nijeriya maza suka bayyana rashin jin dadinsu da wannan al’ada ta Nijeriya ta kin biyan ‘yan wasa hakkokinsu.
Dan wasan Napoli, Bictor Osimhen da tsohon dan wasan Eberton, Bictor Anichebe duka sun nuna rashin jin dadinsu na kin biyan ‘yan wasa mata kudinsu, sannan shi ma dan wasa Odion Ighalo ya bayyana takaicinsa na kin biyansu kudinsu.
Sai dai hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta bayyana cewa za ta biya kudin nan ba da jimawa ba kuma sun yi alkawari da ‘yan wasan cewa sai an gama gasar za su karbi kudadisu, sannan kuma ‘yan wasan sun amince da hakan.