‘Yan bindiga sun hallaka mutane goma sha hudu (14) tare da yin garkuwa da wasu mutane har tamanin da daya (81) a jihohin Sokoto da Katsina.
A kudancin jihar Sokoto, mutum 14 aka kashe aka sace 73 ciki har da mata da yara kanana.
Hare-haren wadanda suka wakana a kauyuka daban-daban da suke karamar hukumar Sabon Birni, Gada da karamar hukumar Goronyo.
Rahotonni sun zo kan cewa kusan a lokaci guda aka kai hare-haren a kuma wuraren daban-daban dukka a ranar Litinin din da ta gabata.
Da ya ke ganawa da Daily Trust, wani basarake a Sabon Birni wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida cewar yankuna uku ne da suke karamar hukumar aka kai harin inda aka kashe mutum 11 a cikinsu.
Ya ce kauyukan sun hada da Gatawa da Dangari da kuma Kurawa.
Shugaban ‘yan Bijilante a Sabon Birni Musa Muhammad da Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Sabon Birni ta kudu a Majalisar Dokokin Jihar, Aminu Almustapha Boza, sun ce an kashe mutumin ne a gonarsa wajajen karfe 5 na yammacin ranar Litinin.
Boza ya ce an yi garkuwa da mutane da dama a wannan harin.
Shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, ya nuna damuwarsa kan harin tare da cewa mutum biyu ne aka kashe a yankin nasa tare da garkuwa da wasu 23 a kauyukan Shinaka da Kagara a ranar Litinin.
Shi ma Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gada ta Gabas a Majalisar Dokokin Jihar, Kabiru Dauda ya shaida cewar mutum sama da 50 ciki har da mata da kananan yara ne aka sace a ranar Litinin.
Kazalika a wani harin da ya faru makamancin wannan, an kashe mutum daya da sace tawas a kauyukan da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a daren ranar Talata.
Wani mazaunin Batsari da ya roki a sakaye sunansa, ya shaida wa ‘yan jarida cewa ‘yan bindigan sun kashe Malam Tasi’u bayan da suka sace mishi dabbobi.
Wata majiya ma ta ce wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai 10 sun kai hari kauyen Shirgi da ke Batsari a safiyar ranar Labara inda suka yi ta harbe-harbe a sama tare da yin garkuwa da wani mutum Alhaji Shuaibu Shirgi.
Sannan ya ce an Kuma sace wasu mata da yara ciki har da yarirai biyu.
Har zuwa lokacin aiko da labarin ba a samu ji daga Kakakin ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah ba.