‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi wa kotu dirar mikiya a yankin Ejemekwuru da ke karamar hukumar Oguta a Jihar Imo, inda suka kashe alkalin kotun, Nnaemeka Ugboma.
Maharan wadanda suka mamaye kotun a kan babura sun kutsa kai cikin kotun, inda suka tasa keyar alkalin zuwa waje sannan suka kashe shi.
- Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta
- Rashin Adalci Tsakanin ‘Ya’ya Yana Jawo Fitintinu (Fatawa)
Kazalika, an tattaro cewa maharan sun yi ta ruwan harsasai a sama daga bisani suka tsere.
Kisan ya haifar da zaman dar-dar da jefa al’umma musamman ma’aikatan kotun cikin zullumi da tashin hankali yayin da al’ummar da ke zaune a kusa da kotun suka tsere don tsira da rayukansu.
Ganau ya shaida cewar alkalin da aka kashe ya kammala karatunsa ne a 1991 kuma haifaffen kauyen Nnebukwu da ke karamar hukumar Oguta.
“An kashe shi ne a lokacin da yake jagorantar zaman kotun wanda ‘yan bindigar da suka zo dauke da bindigogi a kan babura. Babu wani da ya san makasan ko daga inda suka fito.
“Babban abin da ya fi tayar wa jama’a da hankali shi ne ba wanda ya san dalilansu na yin kisan.”
Wani abokin mamacin, Emperor Iwuala ya yi Allah wadai kisan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a.
“Wannan babban abin tir ne. Mun kadu sosai da wannan kisan.”
Shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa a Owerri, Ugochukwu Allinor, ya tabbatar da kisan.
Jin ta bakin kakakin ‘yansandan jihar, Henry Okoye, ya ci tura sakamakon rashin daukar wayar wakilinmu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp