Wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) biyu a Jihar Imo da wasu mutane biyu.
Kwamandan NSCDC a Imo, Mista Matthew Ovye wanda ya tabbatar wa manema labarai hakan a Owerri a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne a unguwar Umulolo da ke karamar hukumar Ngor Okpala a jihar.
- Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 6 A Wasu Birane
- Kotu Ta Ce Ayu Ya Daina Kiran Kansa A Matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP
Ya bayyana sunayen jami’an tsaron NSCDC da suka hada da Sixtus Onwusirike, Mataimakin Sufeto na 2 da Simon Simon, mataimakin Sufeto.
Ya ce an kashe mutanen hudu ne a wani harin ba-zata da aka kai a kasuwar Eke Isu ta al’ummar Umulolo, inda ya ce jami’an tsaro sun mamaye yankin.
Ya kuma ce jami’an NSCDC na tafiya ne a cikin mota lokacin da maharan suka yi musu kwanton bauna suka kashe su.
Sai dai ya shawarci mazauna yankin da su guji daukar doka a hannunsu domin tuni jami’an tsaro ke bincike kan lamarin.
Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan Imo, Mista Henry Okoye, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jihar Imo dai na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da kuma ‘yan ta’addar Biyafara.