Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba a ranar Laraba sun kashe wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda a garin Oyigbo da ke karamar hukumar Oyigbo a Jihar Ribas.
An rawaito cewa jami’an ‘yan sandan da har yanzu ba a tantance ba ‘yan bindigar sun yi masa kwanton bauna ne a yayin da ya ke komawa gida bayan ya tashi daga aiki.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Sanda, Sun Sace ‘Yan China 4 A Wajen Hakar Na’adinai A Neja
- 2023: Bayan Buhari, Dole Dan Kudu Ya Zama Shugaban Kasa – Fayose
Daga baya ya rasu a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a yankin.
Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kisan babban jami’in ‘yan sandan.
Da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Iringe-Koko ta bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Eboka Friday, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan kisan dan sandan.