Akalla mutane takwas ne aka kashe a yammacin ranar Litinin a bataliya ta 83 da ke Barikin Sojojin Ada a Takum hedikwatar karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
Wadanda aka kashe din dai mutanen kauyen Jenuwa Nyafiye ne, wata kabilar Kutep da ke daura da kofar Sojojin. An ce suna dawowa ne daga daya daga cikin wuraren ibadar da ke yankin.
- An Kashe Mutum 3 A Rikicin Kabilanci A Taraba
- Rikicin Addini: An Sanya Dokar Hana Fita A Jihar Taraba
Daya daga cikin sarakunan yankin, Cif Godson Danlami Wasa, wanda ya zanta da wakilinmu ya bayyana cewa ‘yan bindiga ne suka kashe mutanen, ya ce sun shafe tsawon watanni suna ta’addanci a yankin ba tare da jami’an tsaro sun yi nasarar kama su ba.
“Sun mamaye yankinmu da yammacin jiya (Litinin), sun kashe mutanenmu, an kona wasu daga cikin wadanda abin ya shafa, ba za a iya gane su ba, yayin da ‘yan fashin dajin suka kona gidajensu.
Danlami ya kuma bayyana cewa a lokacin da ‘yan bindigar ke kashe wadanda abin ya shafa, maza da mata sun yi ta tururuwa domin tsira yayin da aka bar yara kanana.
“Wannan abu ne mai ban tsoro da ban tausayi yayin da mutane kusan 8 suka kasa tsira daga ruwan harsashi daga ‘yan fashin dajin yayin da wasu da dama suka samu raunuka.”
“Rundunar ‘yan banga da ke yankin sun yi yunkurin yi wa ‘yan bindigar kofar rago sai dai karfin ‘yan bindigar ya fi karfinsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Usman ya kuma ce, bayanan da aka samu kan kashe-kashen sun nuna cewa maharan Fulani ne, ya ce “Kafin sojoji su zo wurin, sai da suka gudu daga yankin, ya ce ‘yan sanda sun mamayi maboyarsu domin kamo su.