Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wasu mutane hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Gambar Sabon-Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmad Wakil, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Bauchi a ranar Lahadi.
- Sojoji Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga, Sun Kashe Da Yawa A Neja
- NIS Ta Samu Gudunmawar Na’urorin Sadarwa Na Miliyoyin Nairori
Ya ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da tsakar daren ranar Asabar kuma sun yi awon gaba da wani mutum guda daya.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike domin kamo maharan.
“Rundunar ta samu kiran gaggawa ne a ranar 22 ga watan Janairun 2022 da misalin karfe 3:45 na dare, wanda ya nuna cewa a wannan ranar da misalin karfe 2:00 na dare wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai farmaki kauyen Gambar Sabon-Layi, inda suka far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
“Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun shirya zuwa wurin da lamarin ya faru karkashin jagorancin DPO din Tafawa Balewa da ke hedikwatar ‘yan sanda ta shiyya, inda aka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Tafawa Balewa domin kula da lafiyarsu,” in ji shi.
A halin da ake ciki kuma, jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki da sahihan bayanan sirri, a ranar Lahadin da ta gabata sun gano wata maboyar makamai da ake zargin ta masu garkuwa da mutane ne a unguwar Tudun Wada da ke Liman Katagum a karamar hukumar Bauchi.
Wakil ya ce ‘yan sandan sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da alburusai masu tarin yawa.