Wasu ’yan bindiga sun kashe masu gadin al’umma guda huɗu a ƙauyen Shurum, da ke Dorowa Babuje, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:56 na daren ranar Juma’a, lokacin da waɗanda aka kashe suke gadin al’ummarsu.
Wani mazaunin yankin, Bulus Bature, ya ce an kashe mutanen ne yayin da suke ƙoƙarin kare al’ummar yankin.
ADVERTISEMENT
Kakakin Ƙungiyar Matasa ta Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar harin tare da kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan kisan tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da abin ya shafa.














