ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Kano Za Ta Jagoranci Jihohin Arewa Wajen Tabbatar Da Nasarar Tinubu —Yusuf

by Muhammad
6 days ago

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa Kano za ta jagoranci jihohin Arewa wajen samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wadda aka kafa domin tattara goyon baya ga Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a faɗin jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Yusuf ya ce Kano, wadda ke da yawan masu zaɓe a yankin Arewa, za ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen mai zuwa.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa za a samu gagarumar fitowar masu zaɓe domin marawa Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Gwamnan ya kuma sake jaddada goyon bayansa ga ƙudirin Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu, yana mai bayyana ƙungiyar A4A a matsayin wata kafa da za ta taimaka wajen ƙarfafa hulɗar siyasa da tattara goyon bayan jama’a gabanin zaɓen.

LABARAI MASU NASABA

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce goyon bayan siyasa ga gwamnati ya kamata ya kasance tare da riƙon amana, kyakkyawan shugabanci da kuma aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

Shettima ya bayyana cewa Arewa ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu, amma ya jaddada muhimmancin samar da sakamako na zahiri da zai tabbatar da cewa gwamnati ta cancanci amincewar da aka ba ta.

Ya amince cewa ’yan Nijeriya na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, yana mai buƙatar gwamnati ta kasance mai sauraron koke-koken jama’a da kuma ɗaukar matakan magance matsalolinsu.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jaddada muhimmancin ba da fifiko ga tsaro, ilimi, rage talauci da samar da damarmakin tattalin arziki ga al’umma.

.

Muhammad
+ postsBio
  • Muhammad
    2027: Matawalle Ya Bai Wa ’Yan Majalisar Zamfara Takwas Motocin Alfarma Kirar SUV
  • Muhammad
    UTME: Ɗalibai 108 Daga 39,000 ’Yan Ƙasa Da Shekaru 16 Ne Suka Cika Sharuddan Shiga Jami’a
  • Muhammad
    ’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Ƙungiyoyin Asiri Takwas da Masu Damfarar ATM Uku A Kogi
  • Muhammad
    Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Ɗan Majalisa Na Watanni 3 Kan Fitar Bidiyon Jan Kunnen Zomo

MASU ALAKA

Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35
Manyan Labarai

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Next Post
Rusau A Kano: Sarki Sanusi Ya Roƙi Abba Ya Biya ’Yan Kasuwar Filin Idi Diyya

Rusau A Kano: Sarki Sanusi Ya Roƙi Abba Ya Biya ’Yan Kasuwar Filin Idi Diyya

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.