Wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun mamayi kauyen anguwar Dandali da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna tare da kashe mutane hudu da jikkata wasu biyar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin hakimin kauyen, Mallam Sunusi Yusuf, ya shaida cewar ‘yan bindigar sun isa kauyen ne da karfe misalin 10:30 na daren ranar Juma’a, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
- Burina Kawo Ci Gaban Da Ba A Taba Tunani Ba A Harkar Fim —Ibrahim Ali (2)
- Yadda Garkuwa Da Dalibai Ke Haifar Da Koma-baya Ga Ci Gaban Ilimi A Arewa
Ya yi bayanin cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar harbe mutum tara gami da yin garkuwa da mutane biyar kafin daga bisani jami’an tsaro suka mamaye su wanda hakan ya janyo suka musayar wuta.
Ko da yake a cewarsa, duk da zuwan jami’an tsaron hakan bai hana ‘yan bindigar yin garkuwa da wasu ba.
“Daga cikin mutum tara da suka harba, hudu nan take suka mutu, yayin da kuma biyar suka samu raunuka.”
Wadanda aka kashe sun hada da Dahiru Tsalha Wawo, Bashir Salisu, Umar Yahuza da kuma Umar Bako. Sannan kuma wadanda suka jikkata su ne; Abubakar Yahuza, Bala Shamaki, Aliyu Ahmed, da Abdullahi Mamuda.
An birne wadanda suka rasa rayukansu a makabartar Hayin Dogo, Unguwar Dankali kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Liman Alhaji Musa Tanko, mai unguwa ne a yankin, ya shaida cewa, al’umma suna cikin firgici da tashin hankali sakamakon yawaitar farmakin da ‘yan bindiga.
“Da farko da ‘yan bindigar na yawan kai hare-hare ne a kauyen Anguwar Dankali, amma yanzu suna mamayar makwafta Wusasa da yankin Kuregu wadanda ‘yan bindiga ke cigaba da kai hare-harensu. Wannan lamarin ya zama abun tashin hankali matuka yayin da ‘yan bindigan ke kara fadada aikace-aikacensu zuwa wasu yankunan,” ya shaida.
Tanko ya yi kiran a dukufa da addu’a domin neman kawo karshen matsalolin tsaro da suke faruwa a yankin.
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yansandan jihar na rikon kwarya, ASP Mansir Hassan, ya yi alkawarin cewa zai tuntubi babban baturen dan sandan yankin, Dan Magaji kuma zai kira daga baya domin bayar da cikakken bayani kan abin da ya faru, amma har zuwa hada wannan rahoto bai kira ba.