‘Yan bindiga sun kashe Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), Muhammad Adamu, a karamar hukumar Barkin Ladi, a Jihar Filato.
Shugaban MACBAN na jihar, Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an kai wa Adamu hari a gidansa da ke Barkin Ladi bayan ya sha ruwa.
- Ba Na Goyon Bayan Dakatar Da Gwamnan Jihar Ribas – Ndume
- Tinubu Ya Yaba Wa Majalisar Dokoki Kan Amincewa Da Dokar Ta-Ɓaci A Jihar Ribas
Babayo ya yi Allah-wadai da kisan, ya kira hukumomin tsaro da su bincika tare da kama waɗanda suka aikata laifin.
Shugaban matasa a yankin, Alhaji Danjuma Ibrahim, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an ajiye gawar Adamu a Asibitin Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi.
Ibrahim ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da aka kai wa Adamu hari, yana tsallake rijiya da baya sai wannan karon aka kashe shi.
“Maharan sun masa harbi da dama sannan suka tsere.
“Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da sojoji, sun kawo ɗauki nan take, sannan muka garzaya da shi asibiti,” in ji shi.
Ibrahim ya ce marigayin mutum ne da ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a yankin, don haka rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Barkin Ladi.
A halin yanzu, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai ce komai kan lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp