Akalla sojoji 26 ne suka mutu, sannan wasu takwas suka samu raunuka bayan da ‘yan bindiga suka yi musu kwantan bauna a jihar Neja.
Bugu da kari, wani kakakin sojin sama ya ce wani jirgi mai saukar ungulu da ya kai dauki ga wadanda suka samu rauni sa ya fado a ranar Litinin a yankin da dakaeun ke yaki da ‘yan bindiga, sai dai bai yi bayani ko wadanda ke cikin jirgin sun tsira da rayukansu ba.
- Juyin Mulki: Hafsoshin Sojin ECOWAS Za Su Cimma Matsaya A Kan Nijar
- Yadda Kasar Sin Ke Hada Hannun Kasa Da Kasa Wajen Inganta Muhallin Duniyarmu Ta Bai Daya
Hafsoshin sojin biyu da suka nemi a sakaya sunayensu sakamakon rashin izinin ganawa da manema labarai, sun ce sojoji 23 ne suka mutu tare da mayakan sa-kai uku, sakamakon mummunan bata-kashi da aka yi a kan hanyar Zungeru zuwa Tegina.
Wata majiya kuma ta ce ‘yan bindigar sun yi asarar dimbin mayakansu.
Ta kuma ce jirgi mai saukar ungulun da ya fadi yana dauke da gwawarwakin dakaru 11 da suka mutu tare da bakwai da suka samu raunuka, tana mai cewa jirgin ya fadi ne sakamakon wuta da ‘yan bindiga suka bude masa.
A wata sanarwa, wani kakakin rundunar sojin sama, Edward Gwabket ya tabbatar da faduwar jirgin, inda ya ce ya kwashi dakarun da lamarin ya rutsa da su ne daga makarantar firamare ta Zungeru, amma ya rikito a kauyen Chukuba na karamar hukumar Shiroro a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
Jihar ta shafe tsawon shekaru tana fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke kisa da kuma sace mutane don karbar kudin fansa, tare da kone gidaje da kuma satar kadarori.