‘Yan bindigar da suka sace almajira 15 a Jihar Sakkwato sun bukaci a biya su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa kafin sakin daliban.
Shugaban makarantar tsangayar da suka sace, Liman Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Talata, ya ce maharan sun kira shi a waya, inda suka bukaci a ba su Naira miliyan 20 domin a sako daliban.
- Boko Haram Ta Sako ‘Yan Gudun Hijira 9 Da Ta Sace A Borno
- Gwamnatin Katsina Za Ta Ciyar Da Marasa Karfi Mutum Fiye Da Miliyan 2.1 A Ramadan
“Sun kira ni da safe yau da misalin karfe 11 na safe, suka umarce ni da na gana da hakimin kauyenmu na ce masa ya tara wa yaran Naira miliyan 20.
“Na je na tattauna batun da hakimin kauyenmu amma har yanzu ba mu kai ga cimma matsaya ba,” in ji shi
A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i, ya ce rundunar tana ci gaba da kokarin kubutar da daliban da aka sace.
“Har yanzu muna kan binciken kauyuka da dazukan da ke kewaye da kauyen domin gano ainihin inda almajiran suke.”
Idan dai ba a manta ba ‘yan bindiga sun sace daliban 15, lokacin da suka kai farmaki kauyen Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada a Jihar Sakkwato da sanyin safiyar ranar Asabar.