Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu dalibai mata biyu a Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, inda masu garkuwa da mutane suka kai farmaki gidan kwanan dalibai da ke Sabon-Gida, a unguwar da ke daura da babbar harabar Jami’ar inda suka yi nasarar daure masu gadin gidan.
- Cutar Da Ke Yi Wa Tumatir Illa Ta Sake Addabar Gonakan Tumatir A Jihar Kano
- DSS Ta Kama Jagoran Inyamurai Da Ya Yi Barazanar Kai IPOB Legas
Daliban biyu da aka yi garkuwa da su, sun hada da Maryam da Zainab.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Leadership Hausa a wata tattaunawa ta wayar tarho, kakakin rundunar ‘yan sandan, Mohammed Shehu, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan kwanan dalibai mata da ke kauyen Sabon Gida a karamar hukumar Bungudu.
Ana cikin haka ne suka daure masu gadin guda biyu tare da kwace musu wayoyinsu kafin su tafi da wadanda abin ya shafa.
“Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sanda ta zo wurin da lamarin ya faru, amma tuni ‘yan bindigar suka gudu tare da wadanda abin ya shafa har yanzu ba a san inda suke ba,” in ji kakakin ‘yan sandan.
“Kwamishanan ‘yan sanda ya kuma kara tura dakarun da za su ceto wadanda abun ya shafa, tare da cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.”
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, kwamishinan ‘yan sandan, Kolo Yusuf, ya bukaci al’ummar jihar da su mara wa ‘yan sandan baya a kokarin da suke yi na ceto daliban.