‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani sabon DPO da aka tura zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safiyar ranar Litinin.
- Kasar Sin Na Adawa Da Duk Wani Yunkuri Na Bata Sunan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
- An Gano Gawar Tsohon Jakadan Nijeriya Da Ya Bace A Amurka
Wata majiya ta shaida wa LEADERSHIP cewa DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kama aiki lokacin da aka sace shi.
Sai dai babu cikakken rahoton lokacin da aka sace shi, shi kadai yake tafiya a cikin abun hawa.
Har yanzu dai ‘yan sanda ba su yi martani ko kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan sace shi ba.
Da aka tuntubi Mohammed Jalinge, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya ce, “Zan yi bincike kan lamarin sannan na baku rahoton abin da ya faru .”