Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da Hakimin Kasuwar Daji da ke karkashin karamar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, Ibrahim Sarkin Fada a gidansa da sanyin safiyar yau Alhamis.
‘Yan bindigar da suka afkawa al’ummar Kasuwar Daji da yawansu, an ce sun nufi gidan hakimin kauyen ne, inda suka yi awon gaba da shi.
- Za A Kammala Aikin Titin Kano Zuwa Kaduna Da Gadar Neja A Ranar 15 Ga Mayu – Gwamnati
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Tsagaita Bude Wuta A Sudan
Mazauna kauyen sun ce ‘yan bindigar sun yi ta harbi don tsoratar da mutanen kauyen.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, CSP Mohammed Shehu, ya tabbatar wa da Leadership Hausa faruwar lamarin a yau ta wata tattaunawa ta wayar tarho.
CSP Shehu ya ce rundunar ‘yan sandan ta tura tawagar bincike don bin sawun ‘yan bindigar da nufin kubutar da Hakimin.
“Eh, gaskiya ne, rundunar ‘yan sandan ta tura tawagar bincike domin ceto shi,” in ji kakakin ‘yan sandan.
An tattaro cewa Hakimin kuma uba ne ga dan majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Anas Sarkin Fada Kaura.
Iyalin dai har yanzu ba su bayar da wani bayani a hukumance ba game da ci gaba ko wani yunkuri na neman tabbatar da kubutar da shi ba.