Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane da dama lokacin da suke sallar Juma’a a kauyen Zugu na Karamar Hukumar Gummi.
Kwamishinan tsaron Jihar, DIG Maman Tsafe (mai ritaya), ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Asabar.
- Fasto Ya Dirka Wa ‘Yar Shekara 12 Ciki A Ogun
- Wasu ‘Yan Siyasa Na Daukar Zaben 2023 Na Ko A Mutu, Ko A Yi Rai –INEC
Sai dai kwamishinan bai fadi adadin mutanen da ‘yan bindigar suka sace ba.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa kai cikin masallacin daidai lokacin da masallata ke sauraren hudubar Juma’a.
Bayan shigarsu suka fara harbi kan mai uwa da wabi, sannan suka debi mutane da dama suka yi awon gaba da su.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke fama da matsalolin ayyukan ‘yan bindiga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp