• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 29 A Kauyen Abuja

by Sadiq
3 years ago
Abuja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu mutane 29 da suka hada da manya maza, matan aure da yara a kauyen Yewuti, mahaifar tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti.

An samu labarin cewa wasu matan aure biyu, Zainab Umar da Aisha Zubairu, sun tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a lokacin da aka kai su cikin daji.

  • Lardunan Sin 8 Sun Samu Karuwar GDP Da Kaso Sama Da 5 Bisa Dari A Rubu’in Farkon Bana
  • Yanzu-yanzun: El-Rufai Ya Nada Sabbin Alkalai 15 Kasa Da Kwana 35 Ya Mika Mulki

Daga cikin wadanda aka sace akwai Idris Mohammed, Abdullahi Zubairu, Sani S. Magani, Peter Modu, Ibrahim Mamman, Yellow Abdulrasheed, Musa Suleiman, Simbiya Ishaku, Sumaiya Ibrahim, Muktari Yunusa da Mohammed Yeluwa da Rahmat Shagari.

Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da, Sumaiya Abubakar Yelwa, Mohammed Yelwa, Maimuna Muhammad, Hussaini Ya Nda Agyana, Hamza Ibrahim, Lantana Yunusa, Nabila Agyana, Rufai Salihu, Nafisa Aminu, Kasimu Adamu, Abako Adamu, Abdulyakin Aliyu, Lukman Aliyu, Rahina Audu, Abdulrazak Usman, Sadiya Usman, Darius Samuel da Japheth Osu.

Wani mazaunin garin Yewuti, wanda ya tsere, Shuaibu Ndako, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da wakilinmu ya ziyarci yankin a ranar Talata, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na daren ranar Talata, inda masu garkuwa da mutane da yawa suka mamaye al’ummar.

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Ya ce masu garkuwa da mutanen da suka raba kan su rukuni-rukuni, sun je gidaje takwas ne a yayin da suke ta harbe-harbe, inda suka tafi da mazauna yankin ciki har da yara da matan aure cikin daji.

“Allah ne ya cece ni. Da na fara jin an buga min kofa, na leko ta taga na ga masu garkuwa da mutane ne. Don haka na buya,” in ji shi.

Ya ce an yi garkuwa da yara biyu da mata biyu a gidansa kafin masu garkuwan su wuce gida na gaba bayan sun bude kofar gidan ta karfin tsiya.

Mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti, wanda ya zanta da wakilinmu a kauyen, ya ce an yi garkuwa da kaninsa Idris da matan yayansa guda biyu da wani yaro a gidansu.

Ya ce masu garkuwa da mutanen da suka yi aiki daga karfe 1 na dare zuwa karfe 3 na dare, sun mamaye gidaje sama da takwas sannan suka yi awon gaba da mutane 29 da suka hada da mata da maza da yara.

Ya ce wasu matan aure biyu sun yi nasarar tserewa daga hannun wadanda suka sace su yayin da aka kai su da sauran wadanda abin ya shafa cikin daji.

Shi ma Etsu Abawa na Yewuti, Alhaji Isyaku Yakubu Yewuti, ya tabbatar da cewa an yi awon gaba da mutanensa 29.

Ya ce an kai mutane biyu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Kwali.

Sarkin wanda ya ce daukacin al’ummar yankin sun firgita da harbin bindiga da masu garkuwa da mutanen ke yi a lokaci-lokaci, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da abin ya shafa da su taimaka masa wajen ceto wadanda aka sace.

Mutanen kauyen Awawa da ke makwabtaka da garin Abaji da Wako suka shiga cikin jama’a don jajantawa iyalan wadanda aka sace.

An kuma ga mafarauta, ‘yan banga, da ‘yan sanda a cikin motocin kirar Hilux guda uku suna shawagi a dajin kauyen.

Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance daga kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, kan sabon harin da aka yi na garkuwa da mutane har zuwa lokacin hada rahoton.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja
Manyan Labarai

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
Manyan Labarai

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
Manyan Labarai

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Next Post
Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin ‘Yansanda 3 A Kaduna

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin 'Yansanda 3 A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja

November 8, 2025
Majalisa Na Binciken Kwangilar Titin Naira Biliyan 1.46 Da Aka Yi Watsi Da Shi A Kaduna

Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna

November 8, 2025
Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

November 8, 2025
An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

November 8, 2025
An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi

November 8, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.