‘Yan bindiga sun sace wasu malaman jami’ar tarayya ta Dutsin Ma da ke jihar Katsina, Farfesa Richard Kyaram da kuma Dakta Hamza.
An rawaito cewa, an sace Mista Kyaram ne tare da dansa, Solomon.
- Daurawa Ya Biya Min Kudin Makarantar Islamiyyar Da Zan Fara Karatu – G Fresh
- Biyan Albashin Da Ƙungiyar Ƙwadago Ke Nema Na Iya Durƙusar Da Nijeriya
Rahotanni sun bayyana lamarin ya faru ne a GRA Dustin-Ma da misalin karfe 1:am na ranar Litinin.
An kuma rawaito cewa, ‘yan ta’addar sun afka GRAn ne da muggan makamai inda suka rika harbe-harbe a sama.
Da aka tuntubi Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai, ya ce, rundunar tana aiki tare da hadin guiwar sauran jami’an tsaro domin ceto wadanda aka sace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp