Duka ‘ya’yan tsohon Akanta-Janar na Jihar Zamfara, Abubakar Bello Furfuri da aka sace sun samu kubuta.
An sake su ne a ranar Litinin, watanni biyar bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
- Kamfanin PowerChina Ya Samarwa Kauyen Lauteye Dake Najeriya Na’urar Samar Da Wutar Lantarki Bisa Hasken Rana
- Gina Al’umma Mai Makoma Ta Bai Daya A Kafar Intanet Na Da Muhimmanci A Zamanin Da Ake Ciki
An yi garkuwa da ‘yan matan ne a daren ranar 5 ga watan Yuni a unguwar Furfuri da ke karamar hukumar Bungudu.
Mazauna kauyen sun tabbatar da cewa an kama mutane kusan 20 a yayin harin kafin jami’an tsaro su isa a lokacin harin.
Daga karshe ‘yan bindigar sun bar ‘yan matan su fice daga dajin bayan an biya makudan kudade a matsayin kudin fansa, kamar yadda wata majiya ta bayyana.
A cikin watan Oktoba ne, Leadership Hausa, ta ruwaito cewar ‘yan bindigar na barazanar aure ‘yan matan idan ba a biya musu bukatunsu ba.