Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta tabbatar da tarar Naira miliyan 10 da ‘yan bindiga suka ci al’ummar garin Gobirawa a karamar hukumar Faskari bisa laifin kashe daya daga cikinsu.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da wannan harajin da ‘yan bindiga suka sanya wa al’ummomin saboda kashe daya daga cikinsu da ke aiki a dazuzzukan Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina, in ji Hakimin garin.
Sai dai kuma an kama wani mai suna Surajo Madawaki mai shekaru 50 da laifin hada baki da ‘yan bindigar.
A cewar sanarwar, ta samu kiran gaggawa a ranar 19 ga watan Oktoba da misalin karfe 9:00 na safe, cewa wani dan ta’adda da ke dauke AK-47 ya kai wa wani matashi mai suna Yahaya Danbai dan shekaru 35 a kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina hari.
An rawaito cewar manomin ya yi jarumta ya kuma yi galaba a kan wanda ya kai masa hari, ya kwace masa makamai tare da kashe dan ta’addan.
Ya ce bayan kashe dan bindigar, ya dauki bindigar AK-47 da aka kwato zuwa gidan Hakiminsa, wanda maimakon ya kai rahoton lamarin ga ‘yansanda, sai dai ya kira wani da ake zargin kwamandan ‘yan ta’adda ne ya mika bindigar AK-47 da aka kwato gare shi.
Bayan haka ne shugaban kungiyar ‘yan ta’addan Hamisu, ya tattara ’yan kungiyarsa, suka kewaye kauyen, suka fito da manomin, suka kashe shi nan take, tare da sanya kudin fansa na Naira miliyan 10 ga al’umma saboda kashe daya daga cikin mambobinsu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, tun bayan faruwar lamarin, Hakimin gundumar, Surajo Madawaki ya boye kansa, har sai da tawagar ‘yansanda suka kamo shi, kuma tuni ya amsa laifinsa, inda ya kara da cewa Maiunguwa, ya musanta dukkan zargin da ake yi masa.