‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane 29 a kauyen Tashar Na-Gulle da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Wani majiya ta shaida wa Leadership Hausa cewa ‘yan bindigar wadanda yawan su ya haura 60 dauke da muggan makamai, sun mamaye kauyen ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Lahadi.
- Karatun Al-ƙur’ani Da Hadda Ce Shi, Yana Taimawa Ginuwar Ƙwaƙwalwa -Gwamnan Kwara
- Ba Irin Wannan Amurkar Kasashen Yankin Gabas Ta Tsakiya Suke Bukata Ba
Ya bayyana cewa, maharan na sanye da kakin sojoji don kada wani daga cikin mutanen kauyen ya ji tsoron su.
“Da isar su kauyen, ‘yan bindigar suka bude wuta suka fara shiga gidajen mutane.
“Sun bukaci mazauna yankin da su tsaya, inda suka bayyana cewa jami’an tsaro ne sun zo don taimaka musu,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Sai dai ya ce tuni rundunar ta aike da tawagarta yankin don tabbatar da tsaro.
A cewarsa, rundunar na kokarin ceto wadanda aka sace a kauyen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp