‘Yan bindiga sun yi garkuwa da akalla masallata uku a wani masallaci da ke yankin Ughelli a Jihar Delta da safiyar ranar Juma’a.
Masu ibadar mutum 11 ne aka ce sun jikkata sakamakon harin gami sanya wa jama’a cikin firgici.
- An Tsinci Gawar Wani Dan Kasuwa Mai Shekaru 37 A Otel A Jihar Bauchi
- 2023: Gwamnatinmu Za Ta Farfaɗo Da Harkar ilimi Da Walwalar Malamai – Atiku
Wani mazaunin yankin da ya zanta da NAN ta waya, ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 6.47 na safe lokacin da mutane ke sallar Asuba a cikin babban masallacin Juma’a na garin wanda ke layin Okoroda a Ughelli.
Ganau din wanda ya ce sunansa Larry, ya kara da cewa, mutane da dama sun kasa komawa barci biyo bayan harbe-harben da maharan suka yi a wajen masallacin.
“Sunana Larry, ni dan Acaba ne a nan Ughelli. Ina rayuwa kusa da babban masallacin Juma’a, wajen karfe 6:45 na safiya kawai sai muka fara jin harbi a masallaci. Saboda firgici, razana kawai muka yi ta lekowa ta taga.”
“A lokacin da harbe-harben ke wakana, mun yi ta jin kukan wasu masu ibada daga cikin masallacin,” a cewar Larry.
A cewarsa, bayan da maharan suka tafi, mutane da dama sun fito domin ganin abubuwan da suka faru.
Ya ce, mutane sun taimaka wajen kwasar wadanda suka jikkata, “Mutum uku kuma an yi garkuwa da su.”
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar’yansandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, mutum 11 ne kawai suka jikkata.
Sai dai bai tabbatar da batun garkuwa da mutum uku ba.
Ya ce, sun fara bincike kan lamarin domin gano abubuwan da suka faru tare da daukar matakan da suka dace.