Wasu ‘yan bindiga a safiyar ranar Litinin sun kai hari a Estate Gwarinpa da ke babban birnin tarayya.
‘yan bindigar sun kai farmakin ne a jerin gidajen a tsakanin karfe 1 na safe zuwa karfe 4 na safe, inda suka yi awon gaba da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani, wani mazaunin garin, wanda ya bayyana sunansa Mohammed ya ce ‘yan bindigar sun samu shiga Estate Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta shaida wa Aminiya cewa lamarin fashi ne ba garkuwa da mutane ba.
Adeh, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce tuni aka tattara ‘yan sanda zuwa wurin domin sanin yadda lamarin ya faru.
Ta yi alkawarin cewa za a sanar da jama’a yadda ya kamata bayan an gano cikakkun bayanai kan lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp