Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifiyar Dan takarar sanatan Kano ta tsakiya a karkashin tutar jam’iyyar APC, Abdulkarim Abdulsalam Zaura, wanda akafi sani da AA Zaura.
Shugaban karamar hukumar Kumbotso ne ya tabbatar da hakan inda yace anyi garkuwa da Baba Laure ne kafin sallar Asuba a unguwar Rangaza dake jihar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano dai har kawo yanzu bata tabbatar da faruwar lamarin ba.
Karin bayani zaizo nan gaba ….
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp