Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabas ta nuna damuwarta kan yadda ‘yan bindigan da jami’an tsaro ke fatattaka daga shiyyar Arewa Maso Yamma ke kwararowa zuwa shiyyar.
Gwamnonin suna masu cewa ana samun nasara sosai wajen kyautata harkokin tsaro a shiyyar, amma suna fuskantar barazanar yawaitar shigowar ‘yan bindiga da jami’ar tsaro ke fatattakar ga Arewa Maso Yamma.
- An Yi Ta Barazanar Kashe Ni Kan Shaidar Katin Dan Kasa Da Rijistar Layuka – Pantami
- Ba A Kashe Dansanda A Harin Da Mahara Suka Kai Ebonyi Ba – ‘Yansanda
A jawabin bayan taron da kungiyar gwamonin Arewa Maso Gabas (NSGF) ta fitar wadda Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karanta wa ‘yan jarida a ranar Juma’a sun yi kira da a hada karfi da karfe da hukumomin tsaro da Gwamnatin tarayya domin dakile wannan matsalar.
Gwamnonin Arewa Maso Gabas din da suka hada da Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri; Bauchi, Bala Muhammad; Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum (Shugaban kungiyar NEGF); Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya; Taraba Darius Dickson Ishaku, da jihar Yobe, Mai Mala Buni sun cimma wannan matsayar ne a lokacin taron su karo na bakwai da ya gudana a jihar Gombe.
Kungiyar ta nuna farin cikinta dangane da aikin hadin guiwa da ake samu tsakanin Gwamnonin jihohin shida wadda sakamakon hakan ana samun cimma muhimman nasarori na kyautata rayuwar al’ummar jihohin.
Gwamnonin sun jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa kokarinsa wajen yaki da matsalar Boko Haram, tare da sa’ayinsa na kyautata harkokin tsaro a shiyyar wadda zuwa yanzu a cewarsu an samu nasarori.
Kungiyar ta ce, raguwar fada tsakanin manoma da Fulani makiyaya abun sha’awa ne.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara azama wajen fatattakar ‘yan garkuwa da mutane da suka addabi wasu sassan kasar nan.
Kungiyar ta nuna damuwarta dangane da karancin samun wutar lantarki a shiyyar Arewa Maso Gabas tare da yin kira da a shawo kan matsalar.
Kan matsalar na wutar lantarki, Gwamnonin sun yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta gaggauta gudanar da aikin samar da wutar lantarki Manbila.
Gwamnonin sun yi nuni da bukatar yin amfani da dimbin albarkatun da ba a yi amfani da su a yankin ba, ta hanyar inganta hada-hadar kasuwanci tare da gudanar da baje kolin kasuwanci da nufin jawo hankalin kasashen waje wajen zuba hannun jari.
Don haka, kungiyar ta bukaci Majalisar ’Yan Kasuwa ta Arewa-maso-Gabas da ta farfado da kasuwar hada-hadar kasuwanci ta Arewa Maso Gabas da kasuwannin kayyayaki don bunkasar da harkokin tattalin arziki.
Kazalika, taron ya jinjina wa Gwamnatin tarayya wajen kafa Jami’ar Kimiyyar lafiya a garin Azare da zimmar shawo kan tulin matsalolin da suke sashin kiwon lafiya, sun kuma yi alkawarin taimaka wa Jami’ar domin cimma manufar da aka samar da ita.
Kungiyar Gwamnonin Arewa sun nuna matukar damuwarsu dangane da ambaliyar ruwa da ta barnata da lalata gidaje, gonakai da gine-ginen jama’a da dama.
Sun nemi Gwamnatin tarayya cikin gaggawa da ta umarci hukumomin da abun ya shafa da su tunkari yankunan da ambaliyar ta shafa domin kai agajin da ya kamata.
Daga karshe sun jinjina wa gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya bisa amsar bakwancin taron, tare da cewa taron nan gaba na kungiyar (karo na 8) da za su yi a ranar Juma’a 25 ga watan Nuwamba zai gudana ne a Maiduguri ta jihar Borno.