Daya daga cikin mawaka kuma Jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wato YUNUSA MUHAMMAD GAYA, ya bayyana wa masu karatu dalilin da ya sa ya tsunduma harkar fim da waka, inda ya yi kira ga Mawaka da Jarumai su guji isar da sakon da bai dace ba. Ya kuma bayyana irin mukaman da ya rike game da wannan sana’a tasa, har da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim da waka. Ga dai tattaunawar tare da wakilinmu YAKUBU FURODUSA GWAMMAJA Kamar haka:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanka…
Sunana Yunusa Muhammad Gaya Shugaban Kundin Muryar Mawakan Arewa.
Ko za ka fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni dan Karamar Hukumar Gaya ne, Kano, Almajiri ne ni bayan na samu haddar Alkur’ani na yi karatun sakandare a Gwale, yanzu ina karatun gaba da sakandare a Sa’adatu Rimi. Na Jagoranci Kungiyar Sha’irai ta Gaya shekara 12, na jagoranci Kungiyar mawalfa ta Gaya shekara 8, na rike ma’aji na kungiyar mawallafa na Jihar Kano. Shekra 2 na rike ma’aji na kundin muryar Mawakan Arewa, yanzu haka ni ne shugabanta na kasa yau shekara 6, na taba samun gwarzon shekara na yabon manzon Allah (SAW) na Jihar Kano.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka?
Na shiga harkar waka ne don isar da sako zuwa ga al’umma, na wa’azantarwa. Haka zalika na shiga harkar fm don fito da martabar al’adata da kuma fadakarwa.
Bayan waka har fim kana yi kenan?
Eh ina yin fim.
Da wanne fim ka fara?
Wani fim ne ‘Me Zai Faru’. Fim din dana fara nawa shi ne;
BA DA NI BA, wanda ya ba da umarni Yakubu Producer. Ma’anar fim din duk wani abin ki jaruman ciki za ka ji na kira ba da ni ba.
Wacce waka ce ta zama bakandamiyarka?
Har yanzu ban fid da bakandamiyar wakata ba.
Nawa ne adadin fina-finan da ka yi da kuma wakoki?
Fina-finaina ba su wuce guda 6 ba, wakoki kuma ba zan iya kidaya su ba duba da mawakan kowanne ban gare ne ni na Hausa.
Za ka yi kamar shekara nawa cikin masana’antar?
Na shiga masana’antar ina da shekara 19.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Hakika an yi gwagwarmaya sosai don harka ce da take bukatar ka san mafi yawan wanda ke da alaka da harkar, sannan harka ce da ke bukatar hakuri.
Wanne irin kalubale ka taba fuskanta game da wannan sana’a taka?
Alhamdulillah kalubale ba za a ce babu ba, musamman a harkar jagoranci duba da kullum burina ya za ayi na samarwa ‘yan kungiyar mafita.
Ya batun nasarori fa?
Ma Sha Allahu na samu nasarori sosai ba zan iya kididdige su ba na kuma yi alaka da manyan mutane da dama.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba mantawa da shi ba?
Abin da ya taba faruwa da ni sanadin harkar, suna da yawa mafi zamammin a rai shi ne kyautar fili da samamin aikin gwamnati.
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar?
Ina da abokai da yawa wadanda kullum ba ma rabuwa.
Da wa ka fi so a hada ka a fim?
Ba ni da zabi a kan wacce na fi so a hada mu a fim.
Mene ne burinka game da waka?
Burina shi ne na ga Al’umma na alfahari da wakokina da kuma fim dina ina so kuma na taimaki na kasa da ni a kan harkar, duk da ba wani girma na yi a ciki ba.
Ya ka dauki harkar waka a wajenka?
Na dauki harkar waka sana’a da kuma harkar fim, sannan wata hanya ce ta kai sako ga al’umma.
Bayan fim da waka kana da wata sana’ar ne, in akwai ya kake iya hada kasuwancinka da kuma sana’arka da fim da waka?
Ina da sana’a na kan iya ware lokacin kasuwaci, ina iya ware lokacin harkar waka ko fim.
To ya batun soyayya fa, ko akwai wadda ta taba kwanta maka a rai cikin masana’antar da har ta kai kun fara soyayya?
Ban fara soyayya ba, amma in hakan ta kama ba zan ki ba, duba da na yi nasarar hada auran ‘yar fim da dan fim ko mawaki da mawakiya ya kai guda 5.
Yaushe za ka yi aure?
Ina da aure matana 2 yanzu haka, ina kokarin karawa in sha Allah.
Wanne kira za kai wa masu kokarin shiga harkar fim?
Kirana ga musu sha’awar shiga harkar shi ne; Kai kokarin ka shigo da kyakyawar manufa.
Wanne kira za ka yi ga sauran abokan sana’arka?
Kirana ga abokan sana’ar mawaka da jarumai, don Allah mu guje wa isar da sakon da bai kamata ba mu kuma kaunaci juna.
Ko kana da wani kira da za ka yi ga gwamnati game da wannan harka taka ta wakoki?
Kirana ga hukuma ta yi kokarin shiga harkar waka ba harkar gudummawa da kara kokarin wajen tantance harkar.
Me za ka ce game da Jaridar Leadership Hausa?
Ina godiya ga jaridar Leadership Hausa,
Allah ya kara daukaka ku dari bisa dari.
Muna godiya
Ni ma na gode.