Rundunar Ƴansandan jihar Jigawa a ranar Litinin ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da aka ceto wasu 18 a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar ta Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Dutse, ranar Litinin.
- Kwale-kwale Ya Yi Ajalin Dalibai 2 A Kano
- Mutane 32 Sun Mutu A Wani Sabon Hatsarin Kwale-kwale A Jihar Taraba
Shiisu ya bayyana cewa rundunar ta samu rahoton lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi a kauyen Kwalgai da ke karamar hukumar Auyo da misalin karfe 10 na dare.
Ya ce kwale-kwalen ya kife ne a hanyarsa ta zuwa kauyen Hadin da ke karamar hukumar.
Shiisu ya kara da cewa kimanin fasinjoji 20 ne ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.
“A ranar Lahadi da misalin karfe 10:00 na dare, rundunar ‘yansandan ta samu rahoton hatsarin jirgin ruwa daga ofishin ‘yan sanda na Auyo, cewa wasu ‘yan kasuwa daga kauyen Kwalgwai da ke karamar hukumar Auyo sun kai kimanin 20, maza da mata sun hau kwale-kwale ya tintsire da su.
“An ce kwale-kwalen ya kife ne a lokacin da yake tafiya ta rafin Kwalgai zuwa kauyen Hadin da ke karamar hukumar,” in ji Kakakin.
A cewarsa, a kokarin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su, an sanar da masunta da wasu matasan garin don kawo ɗaukin gaggawa, a lokacin da tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO suka garzaya zuwa wurin.
Shisu ya bayyana cewa, tawagar ta samu nasarar ceto fasinjoji 18 da ransu, yayin da wasu biyu kuma dukkansu mata aka neme su aka rasa.
“Daga baya, a yau da misalin karfe 6:00 na safe, an tsinci gawar daya daga cikin fasinjojin mata da suka bata mai suna Habiba Ado ta kauyen Kwalgai.
‘Yansandan sun ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya samo asali ne sakamakon igiyar ruwa mai karfi da kuma yawan lodin da direban ya yi har ya kasa tuka kwalekwalen da kyau.
A cewar Kakakin, ana ci gaba da kokarin ganin an ceto ɗaya matar. Shiisu ya kara da cewa an kai dukkan wadanda aka ceto zuwa asibiti domin duba da lafiyarsu.