Ɗan majalisar wakilai, Hon. Ibrahim Usman Auyo, mai wakiltar mazabar Hadejia, Auyo, da Kafin Hausa ta jihar Jigawa, ya yi zargin cewa, wasu ‘yan majalisar tarayya suna karbar cin hancin Naira miliyan 1 zuwa miliyan 3 kafin su gabatar da wani kudiri a wasu lokuta, ko kuma korafe-korafe a lokacin zaman majalisar.
Auyo, wanda aka fi sani da ‘Kamfani,’ ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta inda ya yi magana da harshen Hausa a lokacin da yake mayar da martani kan suka daga ‘yan mazabarsa.
- Sin Ta Kara Yawan Tallafinta Ga Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinu
- ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
Ya musanta ikirarin cewa, wasu ‘yan majalisar suna rubuta kudiri ne saboda bukatun kansu ba na jama’arsu ba, amma ya tabbatar da cewa, akwai masu amsar cin hanci kafin su gabatar da wani kudiri a zauren majalisar.
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi.
“Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, wasu sai sun amso cin hancin kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, kuma dole sai sun bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.”
Dan majalisar ya kuma yi watsi da zarge-zargen da ake masa na cewa, ya yi watsi da shirye-shiryen tallafawa matasa a mazabarsa, inda ya ce galibin ayyukan da yake yi suna amfanar da matasa kai tsaye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp