‘Yan majalisa bangaren marasa rinjaye a Ghana sun nuna adawa kan matakin da Ecowas a É—auka na shirin afka wa Nijar a matsayin wani yunkuri na dawo da mulkin dimokuraÉ—iyya a kasar.
‘Yan majalisar Ghana sun gargadi Shugaban kasar, Nana Akufo-Addo cewa ya dakatar da shirin tura sojojin kasar domin zuwa Nijar.
- Za A Bude Bikin Baje Kolin Cinikayyar Hidima Na 2023 A Satumba
- Kano Pillars Ta Dauki Sabon Dan Wasa Daga Rivers United
“Majalisar dokokin Ghana ba ta tattauna ba kan lamarin kamar yadda sauran kasashe suka yi har ma da daukar mataki, in ji Samuel Ablakwa, wani dan majalisa a kwamitin kula da harkokin kasashen waje.
Ya ce Shugaba Akufo-Addo ba sai ya ji ta baki ‘yan Ghana ba kan lamarin, saboda tura sojoji Nijar ba shi ne mafita ba.
‘Yan majalisar kasar bangaren marasa rinjaye sun ce abin da ya kamata a yi shi ne bin hanyar diflomasiyya da kuma tattaunawa.
“Ba abu mai kyau ba ne tura sojojin Ghana zuwa Nijar domin zubar da jini, kuma muddin ba a yi hankali ba, abin zai sake jefa yankin cikin tashin hankali,” in ji Mista Ablakwa.
‘Yan majalisar sun ce ya kamata a yi amfani da kudin da ake da shi wajen warware matsin tattalin arziki da kasar ke fusknta bayan ciyo bashin $3b daga Asusun IMF maimakon tura sojoji zuwa fada.