Adadin ‘yan majalisar wakilai da ke sa ido a kan kujerar shugaban majalisar wakilai ta 10 a yanzu ya kai tara.
Hakan dai na faruwa ne duk da cewa an sake zaben shugaban majalisar mai ci Femi Gbajabiamila a karo na shida kuma zai kasance a majalisar.
A watan Yunin shekarar 2019 ne dai aka kaddamar da majalisar wakilai mai ci a yanzu, kuma ana sa ran za a kaddamar da majalisa ta 10 a irin wannan wata na shekaran nan.
A ranar Talata ne, Abdulraheem Olawuyi dan majalisa mai wakiltar mazabar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-Ero a Jihar Kwara ya shirya bayyana sha’awar zama shugaban majalisar.
A cewar wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ana sa ran Olawuyi zai bayyana aniyarsa ta neman kujerar ranar Talata a Abuja a hukumance.
Olawuyi wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan ba da agajin gaggawa da shirye-shiryen jinkai, ya ce ya yi tuntubar juna sosai kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin majalisa kuma ya ji dadin yadda ya samu goyon baya.
A cikin sanarwar mai taken, ‘AbdulRaheem ya shiga takarar shugaban majalisar, zai bayyana ranar 4 ga Afrilu a hukumance’, ya ce ya yi imanin cewa ya mallaki kwarewar da ake bukata don samun shugaban mai inganta idan abokan aikinsa suka zabe shi.
Ya ce tsofaffi da sabbin mambobin majalisar za su halarci sanarwar a hukumance.
“Ina mai tabbatar muku da cewa idan aka zabe ni, zan yi kokarin inganta manufofin da za su amfanar da daukacin ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban, kuma za mu yi aiki tare da dukkan bangarorin domin hada kan kasa. Ina matukar fatan haduwa da ’yan’uwana ’yan majalisa tare da bayyana musu ra’ayina, da kuma sauraron ra’ayoyinsu kan yadda za a inganta rayuwar jama’a idan aka zabe ni a matsayin shugaban majalisar wakilai,” in ji Olawuyi.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Mallammadori/Kaugama a Jihar Jigawa kuma mataimakin shugaban kwamitin tsaro na majalisar, Abubakar Yalleman, ya bayyana aniyarsa ta zama shugaban majalisan wakilai a makon jiya.
Mataimakin shugaban majalisar, Ahmed Wase da shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sojojin ruwa, Yusuf Gagdi da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Aliyu Betara da shugaban kwamitin majalisar kan cibiyoyin bincike na kimiyya, Olaide Akinremi da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Benjamin Kalu da kuma shugaban kwamitin sufuri na kasa, Tajudeen Abbas, dukkansu suna cikin wadanda suka nuna sha’awarsu na neman shugabancin majalisar wakilai.
Wase ya fito ne daga Filato a shiyyar Arewa ta tsakiya, Ado-Doguwa ya fito daga Kano a Arewa maso Yamma, Gagdi yana wakiltar Filato a Arewa ta Tsakiya, Betara ya fito daga Borno a Arewa maso Gabas, Akinremi yana wakiltar Oyo a Kudu maso Yamma, Kalu daga Abiya a Kudu maso Gabas, Yalleman daga Jigawa a Arewa maso Yamma, sannan Abbas daga Kaduna a Arewa maso Yamma.
Sai dai kuma kan ‘yan majalisar ya rabu dangane da yankin da za a bai wa shugabancin majalisan a wannan karo.
Tuni dai Wase ya fara ziyartar manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ke fadin kasar nan, a wani bangare na kokarin nuna goyon baya ga burinsa.
Hakazalika, a bangaren majalisar dattawa kuwa, wasu mambobi biyu sun fito fili sun bayyana aniyarsu ta shugabancin majalisar. ‘Yan majalisan dai sun hada da shugaban masu rinjaye, Sanata Orji Kalu da kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Jibrin Barau.
Tsohon shugaban marasa rinjaye, Sanata Godswill Akpabio da shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa, Sani Musa har yanzu ba su bayyana tsayawa takarar shugabancin majalisar ba a hukumance, amma masu goyon bayansu a ciki da wajen zauren majalisar sun yi ta magana a kansu.
Shugaban majalisar dattawa mai ci, Ahmad Lawan zai koma zauren majalisa a majalisa mai zuwa.
Shugabannin jam’iyya mai mulki na kasa sun gana da zababbun ‘yan majalisar tarayya a Abuja a ranar 6 ga Maris, 2023, inda aka tattaunawa a kan shugabancin karba-karba na shiyya-shiyya har zuwa bayan zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da aka gudanar a ranar 18 ga Maris.
APC ba ta gana da zababbun ‘yan majalisar ba makonni biyu bayan kammala zaben.
A halin da ake ciki kuma, dan majalisar wakilai daga Jihar Kano, Shamsudeen Dambazau, ya bukaci jam’iyyar APC ta mika shugaban majalisar dattawa a yankin Arewa maso Yamma, yayin da ya kafe Jibrin ya hau kujerar.
Dambazau wanda ke wakiltar mazabar Takai/Sumaila ta Kano, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a mai taken ‘Majalisar Tarayya ta 10: Me ya sa APC ba za ta bayar da shugabancin majalisan dattawa ga yankin Arewa maso Yamma da kuma dalilin da zai sa Barau Jibrin zai iya zama shugaban majalisar dattawa na gaba, ya lissafo nasarorin da jam’iyyar ta samu a wannan yanki.