RABI’A ABDULLAHI matashiyar daliba mai kokarin ganin ta nemi na kanta domin rufin asiri, ta yi wa ADON GARI bayanin yadda take gudanar da rayuwarta ta fuskar kasuwanci, kalubale da kuma ci gaba har ma da nasarorin da samu da kuma bayar da shawara ga ‘yan mata a kan kauce wa yawan rokon samari. Ga yadda tattaunawarta da wakiliyarmu, BILKISU TIJJANI KASSIM ta kasance:
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki…
Suna na Rabi’a Abdullahi muhammad, an haife ni a Jihar Kano Karamar Hukumar Kumbotso, na yi makarantar Sakandare a Kano na gama 2019 yandu ina Jami’ar Tarayya ta Dutse.
Shin Rabi’a matar aure ce?
A’a ni ba matar aure ce ba
‘Yar kasuwa ce ko ma’aikaciya?
Ni ‘yar kasuwace
Wanne irin kasuwanci?
Ina sayar da Hijjabai da dogayen riguna
Me ya ja hankalinki shiga wannan kasuwanci?
To a gaskiya ni a tunanina zama haka kawai ba zai yiwu ba, ba ka da aiki sai zura ido a na wani kana jiran a ba ka ba gaskiya wannan ba tunani ba ne, sannan duk mai jiran a bashi to gaskiya yana tare da kunsar walakanci domin duk wanda ya hau motar kwadayi to ba inda za ta ajiye shi sai tashar walakanci, da ka yi zaman jiran sai wani ya samo ya baka to ai kin ga gwamma kai ma ka yi hobbasa ka samo naka kin ga ka huta da jiran a baka sai de kai ma ka ba wa wani, sannan kuma ni mai sha’awar saye da sayarwa ce gaskiya shi ya sa.
Meye matakin karatunki ba?
Ni daliba ce a jami’ar Federal Unibersity Dutse, ina shekara ta uku yanzu.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin Kasuwanci?
Eh to gaskiya ba wani kalubale da ya wuce masu karbar kaya bashi kuma su ki cika alkawari, ba wai bashin ne mai ciwo ba kin biyan bashin shi ne mai ciwo a rayuwa, ba za a ce mutum ba zai ba da bashi ba amma kana samu sai ka biya abin da ka dauka komai kudinka, amma sai ki ga wani lokaci ka samu kanka a cikin babu kuma kana bukatar wani abu za ka iya cin bashi amma kana samu sai kabiya.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?
Ina samun budi da rufin asiri Alhamdu lillah sai dai na ce na gode wa Allah.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?
Ya zama idan na zauna ko na samu hutu bana rasa abin yi
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Ta hanyar kafar sada zumunta, kamar Whatsapp, Facebook, Instagram, da dai sauransu.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Abubuwa masu kyau
Ga karatu, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?
Komai ina gudanar da shi cikin tsari komai da lokacinsa, idan kin iya tsara komai, za ki rika gudanar da kome naki cikin sauki sai ki ga kome ya tafi cikin sauki ba tare da kin sha wata wahala ba.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Allah ya yi miki albarka, Ya jikan mahaifiyarki a gaskiya duk wanda ya yi min wannan addu’ar ina jin dadi sosai.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Babban goyan baya da na samu dari bisa dari daga gurin mahaifina sai ‘yan uwana a gaskiya suna goyon bayana sosai suna taimaka min fiye da yadda ba kya zato.
Kawaye fa?
Gaskia ba ni da kawaye
Me kike fiso cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Abin da na fi so cikin kayan sawa ina son atamfa da jallabiya, sai kayan kwalliya gaskiya ni ma’abociyar kwalliya ce dan haka kome ina so.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
Su samu sana’a su daina zaman banza ko rokon samari ko mazaje, saboda shi kansa yawan rokon wani lokaci ya kan janyo muku matsala a rayu wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp