Indabawa
Rahoton Cadre Harmonisé na Oktoba ya yi hasashen cewa akalla mutum miliyan 33.1 a cikin jihohi 26 da FCT za su fuskanci matsalar rashin abinci da abinci mai gina jiki tsakanin Yuni da Agusta 2025.
Hukumar Kula Da Abinci Da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, da Hukumar Samar Da Abinci ta Duniya, da Ma’aikatar Noma da Samar Da Abinci Ta Tarayya, da sauran abokan hulda ne suka gudanar da binciken.
Sauran jihohin da abin ya shafa sun hada da Cross Riber, Enugu, Edo, Abia, Kogi, Nasarawa, Kwara, Ogun, Lagas, Ribas, da FCT.
Rahoton ya nuna cewa wannan adadi ya hada da ‘yan gudun hijira 514,474 a Borno, Sakkkwato, da Zamfara.
Ya bayyana cewa kusan mutum miliyan 25 a fadin jihohi 26 da FCT a halin yanzu suna fuskantar matsalar abinci.
“Muna fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba wanda ya shafi rayuwa da abinci da mai gina jiki a duniya yanku da kasa baki daya.”
Koffy ya ce Nijeriya na fama da tashe-tashen hankula da suka hada da tattalin arziki da suka shafi farashin amfanin gona da noma.
Kayayyaki, abubuwan da suka shafi yanayi kamar ambaliyar ruwa da fari, da rashin tsaro.
Ya bayyana cewa, makasudin taron na CH shi ne nazartar bayanan samar da abinci da kuma abubuwan da ke taimakawa wajen gano yawan jama’a da wuraren da ke fuskantar barazanar karancin abinci mai gina jiki a kasar.
A cewarsa, wadannan tarurrukan kuma suna da nufin ba da shawarar matakan da suka dace don hana ko rage matsalolin abinci da ke faruwa.
Ya ce, “Bincike na CH shi ne mafi aminci, kuma kayan aiki na farko da aka yarda da su don shirye-shiryen jin kai su ne, samar da abinci, da mayar da martani ga rayuwa, da kuma ba da fifikon shirye-shiryen ci gaba.”
Babban Sakataren Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya Temitope Fashedemi, ya yi alkawarin gwamnatin kasar na yin amfani da sakamakon rahoton don jagorantar shirye-shiryen samar da abinci da abinci mai gina jiki a fadin jihohi.
Babban jami’in CH mai kula da shirin samar da abinci na kasa Balama Dauda, ya bayyana manyan abubuwan da ke haddasa matsalar karancin abinci da tsadar kayan masarufi, da ambaliya, da rashin tsaro.